Aliyu Dahiru Aliyu
3 min readSep 16, 2020

--

Akan Jari-Hujja – Aliyu Dahiru Aliyu

A mafi yawan lokacin idan mutum yana matashi, ra’ayin gurguzu (socialism) yafi shiga ransa. Bayan ya girma sai ya koma na jari-hujja (capitalism).

Wannan ba yana nufin hankalin mutum ne ya karu da ya gane fa’idar jari-hujja ba, kawai mutum yana gane biyan bukatar kansa ta fiye masa tsayawa kokarin a samu a raba dai-dai ne.

Tamkar binciken hakikokin falsafa da suka fi yawa idan mutum yana matashi ne. Daga baya bukatun rayuwa sai su dauke tunaninsa ya koma neman kudi da na abinci. Hakan ba yana nufin dena falsafa ci gaba ba ne, yana nufin bukatar ciki tafi bukatar kwakwalwa tasiri ne.

Watakila a lokacin mutum yayi iyali don haka bukatarsa ta biya musu bukata su kadai ita ce a gabansa. Ko kuma bayan girmansa ya samu kasonsa a arzikin kasa don haka baya tunanin sai an raba dai-dai. Daga nan sai ya koma dan jari-hujja.

Falsafar jari-hujja ta kafu bisa tsarin fadadar jarinka dai-dai karfin ikonka. Tana nufin kowa ya zuba karfinsa ya nemi na kansa ba sai wani ya saka masa hannu ba. Idan ka yi kudi ka dauki talakawa su yi maka aiki. Idan ka talauce ka dawo dan aikinsu.

Tana nufin kowace hanya zaka bi ka yi kudi to kawai ka yi matukar bata saba da doka ba. Sabawa da doka a nan bata nufin ka ki kyautatawa. Tana nufin matukar ba sata zaka yi ko laifuka makamantanta ba, to in kaga dama ka tara ninki kudin Dangote ta kowace hanya kuma kada ka taimaki kowa tun da kudinka ne.

Jari-hujja abu ne mai kyau idan aka cire son kai da rashin kyawawan dabi’u da suka yi yawa a cikinta. Ko Adam Smith da ya dabbaka falsafarta shi kansa ya muhimmanta kyautata dabi’u domin saitata. Amma ina! Hakan ba mai yiwuwa ba ne. Idan ta yi nisa, dan jari-hujja yafi ganin kimar riba fiye da duk wasu dabi’u masu kyau.

Jeff Bezos mai kamfanin Amazon da yafi kowa kudi a duniya cikakken dan jari-hujja ne da ma’aikatansa suke kuka da shi saboda yadda suke kukan yana zalintarsu don ribarsa. Kuma da yake an sarkafeka a gurin aiki kana tsoron barinsa, babu yadda zaka iya sai ka ci gaba. Tamkar irin abin da ya rike bayi a da ne. Tsoron idan an gudu ina za a fada.

Mark Zuckerbarg ya siyar da bayanan miliyoyin mutane ga yan siyasa da yan kasuwa domin su juyasu basu sani ba. Don haka kake ganin wasu abubuwa a shafinka na Facebook ka rasa a ina aka samu bayananka har aka san kana nemansu!

Abin da baka sani ba shi ne akwai “robots” da suke biye da kai suna kirga “likes” da “comments” dinka a Facebook suna canko me kake so. Ko da kuwa kallon batsa ne da baza ka so a gane kana yi ba.

Babu ruwan Zuckerberg da kana bukatar a san me kake so ko baka so. Shi bukatarsa riba ce. Wannan idan ma mun tsallake wahalar da ma’aikatansa da aka yi zarginsa da yi kenan. Duka wannan tasirin jari-hujja ne.

Masu jari-hujja suna cewa yinta yana habaka tattalin arziki. Kwarai haka ne, amma na tsiraru. Mafi yawa tafi kara hassada a tsakanin talakan tukuf da kuma mai kudin bishasha.

Jari-hujja tana kirkirar Dangote da yafi kowa kudi a Arewa kuma ta kirkiri Zamfara da aka fi ko’ina talauci a Arewan. Tana sanya bukatar mutum daya ya tara abin da zai ishi dukan duniya. Jeff Bezos yana da kudin da kullum zai iya kashe abin da zai ciyar da mutanen Najeriya baki daya har zuwa shekara 200 basu kare ba!

Da a ce abin zai tsaya iya nan to da sauki. Wani zai ce ai halaliyarsu ce. To amma matsalar shi ne, bisa wannan matakan na “Maslow’s hierarchy of needs”, dan jari-hujja yana tafiya kololuwa domin yayi karfi, haka zalincinsa yana kara karfi domin ya kara samun dukiya.

Daga nan jari-hujja ke fadawa matakin da mutane suke tsanarta. A lokacin zalincinta yake bayyana har a fara yakarta. A lokacin su kuma masu yinta sun riga sun yi karfin da juyasu sai an sha wahala. Za su sayi yan maula da masu kariya. Su sayi sojoji da yan baranda. Daga nan komai zai kare akan talaka.

--

--